Dubban masu adawa da gwamnatin mulkin Soji a Sudan sun ci gaba da zanga-zangar kin jinin Firaminista Abdallah Hamdok sassan kasar, zanga-zangar da shugaban ya bayyana da mafi munin rikici karkashin mulkinsa.
Guda cikin jagororin masu zanga-zangar Ali Askouri ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa a jiya lahadi cewa za su ci gaba da zaman dirshan a wajen fadar shugaban har zuwa lokacin da bukatarsu za ta biya.
Tun daga asabar din karshen makon da ya gabata ne dubunnan al’ummar ta Sudan suka faro zanga-zangar amma ta zaman darshan a tsakar birnin na Khartoum fadar gwamnatin kasar don kalubalantar salon kamun ludayin Firaminista Abdallah Hamdok ta fuskar tattalin arziki da siyasa.
Masu zaman na darshan na bukatar rushe gwamnatin rikon kwaryar ta Sudan tare da Majalisar Kolin kasar da bangaren fararen hular da ke cikin tafiyar gwamnati su jiya baya ga bangaren Sojin.
Zanga-zangar zaman darshan din na zuwa a wani yanayi da aka samu rarrabuwar kai tsakanin mukarraban gwamnatin rikon kwaryar kasar dai dai lokacin da wani bangare ke goyon bayan gwamnatin mai ci a bangare guda kuma dayan sashen ke biyayya ga tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.
A wani labarin na daban ma’aikatar tsaron Sudan ta sanya dokar hana tafiye tafiye kan mambobin kwamitin da ke sanya idanu wajen mayar da kasar kan turbar demokradiyya dai dai lokacin da rikici ke sake tsananta tsakanin bangaren fararen hula dana sojojin da ke mulkin kasar a yanzu tun bayan yunkurin juyin mulkin makwannin baya da bai yi nasara ba.
Wasu majiyoyi sun ce haramcin tafiye-tafiyen ya shafi mutane 11 galibinsu mambobin da ke cikin kwamitin warware manufofin tsohon shugaban kasar al-Bashir, tare da kokarin mayar da kasar turbar demokradiyya.
Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani daga kwamitin ko gwamnatin kasar dangane da dalilin haramcin tafiye-tafiyen, sai dai a baya-bayan nan ana fuskantar takun saka tsakanin bangarorin da ke tafiyar da gwamnatin kasar.
Bayanai sun ce cikin wadanda haramcin tafiye-tafiyen ya shafa har da Mohamed al-Faki wanda ya zargi Sojojin da ke mulki a kasar da fakewa da zargin yunkurin juyin mulki don samun damar ci gaba da kasancewa a madafun iko.
Majiyar da ke zayyano sunayen wadanda haramcin ya shafa ta sanyo sunan Salah Manaa wanda tuni ya bar kasar zuwa birnin Alqahira na Masar.
Masana dai na kallon haramcin tafiye-tafiyen kan mutane 11 baya kan ka’ida la’akari da yadda ya fito daga wani kwamitin tsaro na musamman maimakon Ofishin babban mai shigar da kara na gwamnati da aka saba gani bisa tsarin doka.