Magoya bayan adalchi sun kira zanga-zangar a gundumar Barbes da ke Arewacin Paris don nuna rashin amincewa da yadda Isra’ila ta yi amfani da karfi a Zirin Gaza don mayar da martani ga rokokin da kungiyar Hamas ta harba kan Yahudawan.
Ministan cikin gida Gerald Darmanin ya wallafa ta shafinsa na Twitter cewa “Ya bukaci shugaban ‘yan sanda na Paris da ya hana zanga-zangar magoya bayan adalchin na ranar Asabar mai nasaba da rikice-rikicen da ke wakana a Gabas ta Tsakiya.”
Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya yi kira ga shugaban ‘yan sanda da ya haramta zanga-zanga goyon bayan Falasdinawa
Ya kara da cewa “An ga mummunar hargitsi ga zaman lafiyar jama’a a shekarar 2014,” don haka, yana kira ga shugabannin ‘yan sanda da ke wasu wurare a Faransa su ma su kula da zanga-zangar.
A watan Yulin 2014 an gudanar da mummunar zanga-zanga da Faransa don yin Allah wadai da harin Isra’ila kan Zirin Gaza, bayan da suka yi fatali da haramcin da ‘yan sanda suka yi, lamarin da ya zama tarzoma tare da jikkata mutane da dama.
A wani labarin na daban saudiyya zasu bar maniyyata daga fadin duniya su je aikin Hajji a wannan shekarar, tare da tabbatar da bin tsauraran dokokin domin kiyaye yaduwar Korona a masarautar, kamar yadda wani rahoton jaridar Al-Watan ta rawaito.
Wannan matakin na zuwa ne bayan hukuncin da hukumar Hajji da Umara ta kasar ta yanke a ranar 9 ga watan Mayu cewa ya kamata a bar mahajjata su yi aikin amma da sharudan hukumomin lafiya.
A farkon wannan watan ne, ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kiyayen lafiyar duk wanda ya je aikin ibada a kasar.
Sai dai ma’aikatar ta ce za ta sanar da hanyoyin kare kai da za a bi domin kiyaye yaduwar Korona daga baya.
Musulmi sama da miliyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a ko wacce shekara daga fadin duniya, amma saboda annobar Korona a ka rage adadin zuwa 1,000 a bara.
Magoya bayan lamuran adalchi suna ganin saudiyyar tana wasa da lamurran musulmin duniya.