Shugaban LaLigar Spain, Javier Tebas, ya yi ikirarin cewa Real Madrid tana da isassun kudin da za ta iya sayen Kylian Mbappe da Erling Haaland a shekara mai zuwa.
Real Madrid din dai ta gaza a kokarin da ta yi ta yi na sayen Mbappe daga Pafris Saint Germain a watan da ya gabata.
Har sai da kungiyar ta LaLiga ta ta yi tayin bada fam miliyan 137 amma PSG ta yi fatali da wannan tayi.
Madrid ta kara kudin zuwa fam miliyan 145 har da wasu jerin kari da suka kai fam miliyan 9 jimilla, amma duk da haka PSG din ta ce ba ta san wanna zance ba.
A ranar karshe ta kasuwar hada hadar ‘yan wasa, Madrid ta kara tayin baiwa PSG fam miliyan 189 a kan Mbappe din amma sai ta ji shuru daga kungiyar ta kasar Faransa.
A wani labarin na daba Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba kowane wasa bane Cristiano Ronaldo zai buga a tawagar Manchester United, yana mai cewa yana kokari ne ya alkinta tare da tattalin lokacin da dan wasan gaban kada a samu matsala.
Sai dai kocin dan kasar Norway ya zake cewa fa lallai ba kowane wasa ne Ronaldo zai buga ba, saboda kada ya samu matsala, duba da cewa shekarunsa 36 ne.
Solskjaer ya ce gaskiyar lamari Ronaldo yana matukar kula da kansa da lafiyarsa, saboda haka ya san ko da ya samu matsala zai murmure ba da dadewa ba, amma kamata ya yi a yi taka tsantsan.