Madagascar; ‘Yan Sanda Sun Kashe Masu Zanga-zanga 14.
Rahotanni daga Madagascar, na cewa mutane kimanin 14 ne suka mutu lokacin da ‘yan sanda suka bude wuta kan wasu masu zanga zanga a kasar.
Bayanai sun ce daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin ‘yan sanda a yankin Ikongo dake kudancin kasar.
Masau zanga zangar dai na masu bukata ne a sako wasu mutane hudu da ake zargi da sace kananan yara zabiya.
Daga bisani ne kuma ‘yan sanda suka budewa masu zanga-zangar wuta, inda suka kashe a kalla mutane 14 tare da jikkata wasu 28, kamar yadda wasu majiyoyi a yankin suka shaidawa kamfanin dinlancin labaren AFP.
Shugaban kasar Madagascar ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, ya yi matukar bakin ciki da jin wannan labari, inda ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da yin alkawarin gudanar da bincike kan lamarin.
Masu fama da larurar zabiya, na fsukantar hare hare har ma da kisan kai a Madagaska, inda wasu alkaluman da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya fitar a watan Maris sun nuna cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, an aikatar da laifuffukan ga zabiya fiye da sau 10.