Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine zai dauki dogon lokaci sakamakon yadda al’amura ke tafiya.
Macron ya shaidawa taron bikin nuna amfanin gona cewar ya dace jama’ar kasar su shirya tinkarar matsalar da zata biyo baya.
Shugaban na Faransa ya katse halartar bikin baje-kolin amfanin gonar wajen komawa fadarsa domin tinkarar rikicin dake gudana a Ukraine.
Macron ya ce yaki ya koma nahiyar Turai, kuma shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya haifar da shi akan mutanen Ukraine wadanda da ke bijirewa kasar sa da kuma rungumar kasashen Turai.
Shugaban ya sake kiran wani taron majalisar ministocin sa da na tsaro na gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a Ukraine.
Takunkumin da aka kakabawa Rasha sakamakon wannan yakin zai yi matukar illa ga bangaren cinikin barasar da Faransa ke sarrafawa, yayin da shugaba Macron ke Nazari akan yadda za’a taimakawa bangaren.
Shugaba Macron ya taka rawa sosai wajen hana barkewar yakin ta hanyar diflomasiya, inda ya dinga kai gwauro yana kai mari tsakanin shugabannin Rasha da Ukraine da Jamus da kuma Amurka domin ganin an kaucewa tashin hankalin.
A wani labarin na daban Akalla mutane sama da 500 suka shiga zanga zangar adawa da gwamnatin sojin Chadi a birnin Ndjamena, yayinda su ke sukar kasar Faransa da su ke zargin cewar ta na daurewa jagorancin Sojin kasar gindi.
Masu zanga zangar suna dauki allunan da ke nuna cewar, ‘a kawo karshen cin zarafin da Yan Sanda ke yi’, ‘Faransa ta fita a Chadi’, yayin da suke fadin ‘Bamu yarda da Faransa ba’, ‘muna goyan bayan Rasha’ da kuma ‘muna bukatar Rasha kamar yadda take a Mali.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace an ga matasa na jan tutar Faransa a kasa daga cikin mota da kuma taka ta, yayin da wasu ke daga tutar Rasha da Chadi.
Max Loalngar, mai magana da yawun Wakit Tamma ya bayyana cewar sojoji ne suka haifar da matsalar Chadi lokacin da ya ke magana da taron mahalartar zanga zangar, yayin da yayi zargin cewar Faransa na hada baki da sojin wajen hallaka su.
Masu zanga zangar sun kuma bukaci gudanar da taron kasa na gaskiya wanda zai kaiga lalubo hanyar warware rikicin kasar.