Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi abokiyar takarar sa Marine Le Pen saboda mu’amala da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya musanta cewar ya goyi bayan Rasha na mamayar Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ko da ya ke Macron bai furta sunan Le Pen ba, yana nuni ne gare ta saboda yadda Putin ya karbe ta a shekarar 2017.
Le Pen dai ta nesanta kanta da shugaba Putin bayan da ya mamaye Ukraine, tana mai cewa ya sauya daga mutumin da ta hadu da shi a shekarar 2017.
Macron ya ci gaba da dasawa da Putin ko bayan mamayar Ukraine da kasarsa ta yi a 24 ga watan Fabrairu, amma fa ya ce ya yi haka ne bisa bukatar hakan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya mika masa.
A wani labarin na daban Gwamnatin kasar Jamus ta ce abu ne mai wuya su iya katse cinikayyar iskar gas tsakaninsu da Rasha saboda takunkuman da Turai ta kakabawa kasar ta gabashin Turai kan mamayarta a Ukraine.
A cewar Lindner ba Jamus kadai ba, hatta sauran kasashen Turai da ke kiraye-kirayen basu san makomarsu ba idan har suka amince da katse cinikayyar makamashin da Rasha, domin kuwa har yanzu hasashensu bai kai ga gano kasar da za ta maye musu Moscow wajen wadata su da makamashi ba.
Ministar kudin na Jamus Christian Lindner ya ce katse cinikayyar zai fi yiwa Turai illa fiye da Rashan kanta, wanda ke nuna batun daukar matakin bai taso ba.
Kasashen Turai na son katse cinikayya tsakaninsu da Rasha don ladabtar da kasar kan abin da ta ke aikatawa a Ukraine tun karshen watan Fabarairun da ya gabata.