Shugaba Emmanuel Macron ya taka leda a wani wasa da aka shirya don tara kudin bayar da agaji cikin daren jiya alhamis a Faransa.
Wasan dai ya gudana ne a Poissy da ke wajen birnin Paris, kuma bangaren tawagar ta Macron ya samu bugun fenariti wanda shugaban magoyin bayan kungiyar kwallon kafa ta Marseille ya doka tare da nasarar zura kwallo.
Bayan nasarar zura kwallon ta Macron dai an kaure da sowa a filin wasan wanda ya samu tarin ‘yan kallo, ciki har da mai dakin Macron wato Brigitte mai shekaru 68.
Macron wanda ya doka kwallo lokacin yana dalibi a matakin jami’a kwararre ne kuma a fagen kwallon tennis.
Gabanin wasan dai Macron ya sanar da shirin zuba yuro miliyan 200 don sake bunkasa filin wasan da kasar ke shirin karbar bakoncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympic a shekarar 2024.
Macron dai ba shi ne shugaba na farko da ya doka tamaula don tattara kudin agaji ko kuma farantawa al’ummar kasarsa ba, domin kuwa shugaban Turkiya Recep Dayyib Erdogan ya kware wajen doka irin wadannan wasannin yayinda takwaransa na Rasha Vladimir Putin shi ma yakan doka wasannin baya ga kwallon kafa ma har da Hockey da ninkaya da kuma kokwawar Judo data Sambo
A wani labarin na daban kocin Faransa Didier Deschamps ya zubar da Samir Nasri na Manchester City cikin jerin ‘yan wasa 23 da ya zaba wadanda zasu wakilci kasar a gasar cin kofin Duniya a Brazil. A 2010 ma Nasri ba ya cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Afrika ta kudu.
Kusan ‘Yan wasa sama da 20 a tawagar ta faransa zuwa Brazil matasa ne da Deschamps ya zaba.