Macron ya soki manufar Le Pen ta haramta wa matan Musulmi yin lulluɓi.
Shugaba Emmanuel Macron ya yi saɓani da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen kan shirinta na hana mata yin lulluɓi a bainar jama’a, yayin da yake neman ƙuri’un Musulmi a zagaye na biyu na zaben shugaban Faransa.
A ranar 24 ga watan Afrilu za a yi zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa inda Marine Le Pen ke neman haifar da wani yanayi mafi girma a tarihin siyasar Faransa idan har ta doke Emmanuel Macron.
Har yanzu Le Pen ba ta janye manufarta ba ta haramta hijabi, inda ta ce za ta ci tarar duk matar da ta saka hijabi a bainar jama’a a Faransa idan har ta ci zaɓe.
Sai dai Macron ya ce babu wata ƙasa a duniya da ta haramta sanya hijabi, yana mai jefa tambaya ga Le Pen cewa: Kina son ki zama ta farko ne?
Ya tattauna da wasu mata musulmi da suka shaida masa cewa sanya mayafi zaɓi ne nasu ba tursasa masu aka yi ba.
Macron ya san muhimmancin ƙuri’un Musulmin Faransa miliyan biyar, waɗanda aka ƙiyasta sun kai kusan kashi tara na yawan al’ummar ƙasar.
Sakamakon wata ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifop pollster ta nuna cewa kashi 69 na Musulmi sun zaɓi Jean-Luc Melenchon ne wanda ya zo na uku a zagaye na farko. Yanzu kuma Macron na neman yadda zai mamayi ƙuri’un a zagaye na biyu.
Macron a baya ya fuskanci bore daga Musulmi a ƙasashen duniya kan matakan gwamnatinsa na kallon Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.