Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da shugabannin ‘yan adawa domin kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan rashin samun rinjaye a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, bayan da ya ki amincewa da tayin murabus din da firaministar kasar ta yi.
Macron ya gana da masu ra’ayin rikau, da kuma wasu shugabannin jam’iyyu na masu tsassauran ra’ayi irin su Marine Le Pen, yayin da yake neman mafita ga wani mawuyacin hali da ke barazanar jefa wa’adinsa na biyu cikin rikici watanni biyu bayan samun nasara a zaben shugabancin kasar.
Kazalika kallon gurguncewar siyasa da irin nasarorin da ‘yan adawa irin su Le Pen suka samu, shi ma ya sanya ayar tambaya game da shugabancin Macron a nahiyar Turai, yayin da yake kokarin ci gaba da taka rawa wajen tunkarar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Firaministar Faransa Elisabeth Borne, wadda wasu manazarta ke zargin ta da hannu wajen gudanar da yakin neman zabe, ta mika wa Macron tayin murabus din ta, amma shugaban kasar ya ki amincewa da hakan.
Macron ya fara tattauanwar ne da Christian Jacob, shugaban jam’iyyar ‘yan mazan jiya, wato jam’iyyar da ta samu koma baya a watannin ‘yan watannin da suka wuce, amma a halin yanzu shugaban kasar zai iya nemansa don hada kai wajen samar da rinjaye a majalisar dokokin kasar.
A wani labarin na daban ministan Shari’ar Amurka Merrick Garland, ya lashi takobin taimaka wa gwamnatin Ukraine wajen shigar da karar Rasha da ake zargi da aikata laifukan yaki a kasar ta Ukraine.
Tuni Mista Garland ya sanar da kafa wani kwamiti karkashin shugabancin Eli Rosenbaum, kwararran lauyan nan da ya jagoranci Amurka har ta yi nasarar gano tare da tasa keyar ‘yan Nazi da suka aikata laifukan yaki.
Garland ya ce, Amurka da sauran kasashen duniya sun ga hotuna masu tayar da hankula da ke nuna irin girmar barnar da Rasha ta yi a Ukraine, yana mai cewa, babu maboya ga miyagun mutane kuma za a gurfanar da su.
Ministan Shari’ar dai ya yada zango ne a Ukraine akan hanyarsa ta zuwa birnin Paris domin halartar wani taro tsakanin Amurka da kasashen Turai kan lamurran da suka shafi shari’a da kuma harkokin cikin gida.
Kusan watanni hudu kenan da fara yakin Ukraine, yayin da gwamnatin kasar ta bayyana cewa, ta tattara dubban hujjoji kan zargin da ake yi wa Rasha na aikata laifukan yaki a kasar.