Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya soke tafiya zuwa Mali don ganawa da shugaban rikon kwaryar kasar Kanal Assimi Goita, biyo bayan sanar da sabbin matakan yaki da cutar Korona da gwamnatinsa ta yi a jiya.
Macron ya kuma kamata ya kai ziyarar kirsimeti ga sojojin Faransa da aka girke a kasar dake yankin Sahel domin murkushe ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi.
Tun a shekarar 2013 Faransa ta jibge dakarunta a Mali don su taimaka wajen yaki da ayyukan ta’addanci daga mayaka masu ikirarin jihadi.
A wani labarin na daban shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai gana da shugabannin kasashen yankin Sahel yau juma’a don tattaunawa kan barazanar tsaron da yankin ke fuskanta sakamakon tsanantar hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.
Tun a jiya Alhamis fadar Elysee ta sanar da shirin ganawar shugabannin a wani bangare na taron na yau, ganawar da ke zuwa dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Mali da Faransar wadda ta yi mata mulkin mallaka musamman bayan juyin mulkin baya-bayan nan da Paris ta kalubalanta.
Babu dai cikakken bayani ko Firaminista Choguel Kokalla Maïga na Malin na cikin jerin shugabannin da Macron zai gana da su a taron na yau.
Alaka ta kara tsami tsakanin kasashen biyu bayan musayar zafafan kalamai musamman bayan da Paris ta fara janye dakarunta da ke taimakawa a yakar ta’addanci da kuma yunkurin Bamako na daukar Sojin hayan Wagner daga Rasha don taimaka mata fatattakar ayyukan ta’addanci.
Ganawar ta Macron da kassahen na Sahel 3 na zuwa a wani yanayi da ayyukan ta’addanci ke ci gaba da tsananta a ilahirin kasashen 3 inda ake rasa rayukan dakaru a kusan kowacce rana baya ga daruruwan fararen hula da hare-haren ta’addancin kan shafa.