Wasu fitattun mawaka da masu shirye fina-finai na Faransa kimanin 500 sun sanar da goyan bayan su ga shugaban kasar mai ci Emmanuel Macon a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar dake tafe, suna masu yin tir ‘yar ‘Yar takara jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi Marine Le Pen sa suka kira ta da mai kyamar baki.
Yanzu haka ‘yan takarar biyu sun zafafa yakin neman zabe don jan hankalin magoya bayansu da na sauran ‘yan takara da suka gaza kaiwa zagaye na biyu, masamman Jean Luc Melanchon da ya zo na uku a zagayen farko na zaben.
A wani labarin na daban Yayin da ya rage kwanaki 10 gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa, manyan ‘yan takara biyu dake shirin fafatawa Emmanuel Macron da Marine Le Pen na ci gaba da zawarcin ‘yan bangaren hagu, na masu sassaucin ra’ayi wadanda kuri’unsu ke da mahimmaci a zaben.
Yayin da yau yake gangami a Havre dake arewa maso yammacin kasar, tungar tsohon Firayimminista Edouard Philippe.
Ita kuwa Marie Le Pen ta jam’iyyar RN mai tsatsauran ra’ayi, ta zayarci Avignon mai tazarar kilomita 800, da inda abokin karawarta Macron ke ziyara a Kudancin Faransa, nan ma daya daga cikin manyan mazabu ne da suka baiwa Melenchon nasarar zama na uku, ko da yake ya yi kira ga magobaya bayansa da kada su baiwa Le Pen ko da kuri’a daya, duk da cewa yankin masu tsatsauran ra’ayi ne bisa al’ada.
Ga ‘yan takarar da ke neman shiga Fadar Elysée, samun goyan bayan dan takarar jam’iyyar LFI na ‘yan mazan jiya Jean-Luc Mélenchon nada mutukar muhimmaci, saboda matsayin sa na uku a zagayen farko a ranar Lahadi da kashi 22% na kuri’un da aka kada, biye da Marine Le Pen da ta samu sama da kashi 23 da kuma Emmanuel Macron da ya samu sama da kashi 27.