Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon: Isra’ila ce ke da alhakin halin da ake ciki a Falasdinu
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Lebanon ta fitar, ta yi Allah wadai da zaluncin da gwamnatin sahyoniyawan take yi kan al’ummar Falastinu, musamman ma hare-haren wuce gona da iri kan sansanin Jenin na baya-bayan nan, tare da dora alhakin tabarbarewar al’amura a yankunan Falastinawa da suke mamaya na gwamnatin sahyoniyawa.
Sanarwar ta kuma ce: Isra’ila ita ce ke da alhakin kara ruruwa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Falasdinu da yankin Zirin Gaza, da kuma ci gaba da tozarta masallacin Al-Aqsa da Quds Sharif.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NNA cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Lebanon ta taya al’ummar Falastinu murnar samun nasarar kare filayensu da kadarorinsu da wuraren ibadarsu ta hanyar amfani da duk wata hanya da ta dace sannan ta jaddada cewa: Rashin zaman lafiyar al’ummar Falastinu ya samo asali ne daga matakin da Isra’ila ta dauka na ruguza bangarorin biyu.
warware matsalar kasa da kasa da kuma rage hankalin kasashen duniya kan batun Falastinu da kuma manufofin wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan…