Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Gayyaci Jakadan Kasar Sweden Dake Tehran.
A ci gaba da cece kuce da ake yi game da tsare wani dan kasar iran da aka yi a kasar Sweden , ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta gayyaci jakadan kasar Sweden dake nan birnin Tehran domin nuna rashin amincewarta da matakin da ta dauka,
A jiya lahadi ce aka yi zaman kotu don ci gaba da shari’ar da ake yi wa Nuri wani dan kasar iran a kasar Sweden inda alkalin kotun ya yanke masa hukumci daurin rai da rai a gidan yari .
Mataimakin ministan kuma darakata janar na yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi Allah wadai da tsarewa da kuma shri’ar da akai yi wa Hamid Nuri bisa tasirantuwa da hujjojin karya da kungiyar Ta’adda ta munafukai MKO ta gabatar, da kuma yanayi na nuna adawa da jamhuriyar mulunci ta Iran
Har ilayau yayi kira da a kawo karshen zaman kuton na Sweden na wasan kwaikwayon siyasa kuma a sake Nuri daga inda ake tsare da shi.
Anasa bangaren jakadan na kasar Swedin Mattias Lentz ya fadi cewa zai isar wad a mahukumtan kasar matsayin Iran kan wannan hukumci kuma da sanuu zai sanar da Ma’aikatar harkokin wajen Iran Amsar da aka bayar.