Wasu ma’aikatan asibitin a kasar Amurka sun zabi kora daga bakin aikinsu mai makon ayi masu allaurar rigakafin annobar korona saboda shakku da suke da ita.
Bridges na daya daga cikin ma’aikatan kusan 150 da aka kora ko suka yi murabus maimakon amincewa da tsarin Methodist, dake zama na farko a Amurka da ya tilasta yin rigakafi.
Inda Kimanin wasu ma’aikata dubu 25,000 suka bi tsarin asibitin wajen karban allurar.
A wani labarin na daban shugabannin kasashen Duniya da ke halartar taron yaki da annobar covid-19 a Amurka sun goyi bayan karfafa shirin COVAX da nufin wadata duniya da alluran rigakafin cutar ba tare da fifita mawadatan kasashe akan matalauta ba.
A kokarinta na ganin an yiwa kowanne dan adam allurar rigakafin a sassan Duniya, Amurka ta sanar da kara yawan allurai miliyan 500 ga kasashe mabukata don taimaka musu yaki da cutar ta covid-19 dukkaninsu karkahsin shirin na COVAX.
Itama Sweden ta sanar da bayar da tallafin dala miliyan 243 ga shirin don kara yawan alluran da ake shirin samarwa tsakanin 2021 zuwa 2022.
A bangare guda kungiyar Tarayyar Turai da Italy da Spain akan gaba baya ga Denmark sun alkawarta bayar da tallafin karin alluran rigakafin ga shirin na COVAX yayinda Japan ta yi makamancin alkawarin.
Da ya ke gaban taron shugaban hadakar GAVI Jose Manuel Barroso ya ce shirin na COVAX ya samu gagarumin tagomashi irinsa na farko tun farowarsa, yayinda shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bukaci shigowar kasashen nahiyar masu karfin tattalin arziki don taimakawa a yaki da cutar.
Shi kuwa shugaban hukumar Lafiya ta duniya Dr Tedros Adhanom Gebreyesus godiya ya mika ta musamman ga shugaban Amurka Joe Biden da ma sauran manyan shugabannin duniya game da tallafawa shirin na COVAX don kammala yakar cutar ta covid-19 daga ban kasa.