Siterekan na Chelsea a zanatawarsa da sashen wasanni na CNN ya ce baya tunanin iyakar durkuso zai amfanar a yaki da matsalar.
Dan wasan na Belgium ya ce kusan kowanne wasa sai sun gamu da wani sabon salon nuna wariya, walau sun yi nasara ko akasin haka, wanda ke nuna akwai bukatar hada karfi don magance matsalar.
Tun daga bara ne ‘yan wasan Firimiya ke durkuson gwiwa dayar a farkon kowanne wasa da nufin yaki da matsalar ta nuna wariya, said ai wasu ‘yan wasan na ganin hakan baya amfanarwa.
A wani labarin na daban hukumar FIFA ta haramtawa Hungary baiwa magoya bayanta damar shiga kallon wasanninta har guda 2 a jere, matakin da ke matsayin hukuncin wariyar da ‘yan wasan Ingila suka fuskanta a kasar yayin wasannin neman gurbi a gasar cin kofin duniya tsakanin kasashen biyu ranar 2 ga watan Satumba.
Sanarwar FIFA da ke cin tarar hukumar kwallon kafar ta Hungary yuro dubu 158 ta kuma bayyana cewa hukumar baza ta lamunci kowanne nau’in nuna wariya a kwallo ba.
Ita kanta Uefa ta yiwa hukumar kwallon kafar ta Hungary makamancin hukuncin ta hanyar cin tarar ta yuro dubu 85 da kuma hana ‘yan kallo shiga fili a wasanni 3 duk dai dangane da nuna wariyar amma wannan yayin wasannin Euro 2020 da suka gudana cikin watan yuni zuwa Yuli.
‘Yan wasan da suka gamu da nuna wariyar sun hada da Raheem Sterling da kuma Jude Bellingham wadanda magoya baya suka riga jifa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci yayin wasan kasashen biyu a Puskas Arena wanda Ingilar ta yi nasara kan Hungary da kwallo 3 da nema.