Luguden wuta ya sanya Falasdinawa cikin makokin mutuwar mutane 10 ‘yan iyali guda da hare haren haramtacciyar kasar Isra’ila suka kashe.
Ma’aikatan lafiya a yankin Falasdinawa sun ce mutane 10 daga iyali guda sun gamu da ajalinsu a safiyar Asabar dinnan biyo bayan luguden wuta da sojin saman Isra’ila suka yi a yankinsu.
‘Yaya 8 da mata 2, duk daga iyalin Abu Hatab sun mutu a wani bene mai hawa 3, da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ya ruguje bayan harin da Isra’ila ta kai.
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a wasu wurare a yankin Zirin Gaza a cikin dare, kwana guda bayan mummunan luguden wuta a yankin Yamma da Tekun Jordan a yayin da adadin wadanda suka mutu ke dada karuwa.
Duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na kwantar da hankula a rikicin da aka shafe kwanaki 5 ana yi tsakanin Israila da mayakan Hamas a yankin, sojin saman Isra’ilar sun yi ta luguden wuta a cikin dare, a yayin da kungiyar Hamas ke ci gaba da aikewa da rokoki zuwa yankin Yahudawa.
Adadin wadanda suka mutu a yankin na Gaza ya kai 126, ciki har da yara 31, a yayin da ya zuwa yanzu wadanda suka jikkata sun kai 950.
A wani wani labarin mai kama da wannan rundunar sojin Isra’ila ta ce makaman roka akalla dubu 1 da 500 mayakan Falasdinawa suka harba cikin kasar a cigaba da fadan da suke gwabzawa biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu a birnin Kudusn a karshen makon da ya gabata.
Rikicin tsakanin Isra’ila da Falasdinawa dai na cigaba da yin muni musamman a jiya Laraba, duka da kiraye-kirayen hukumomin kasa da kasa kan kawo karshensa.
A ranar Laraba dai hotunan bidiyon dake yawo a kafafe daban daban sun nuna yadda luguden wutar da jiragen yakin Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a birnin Gaza yayi sanadin rushewar wani kafataren gini mai benaye da dama da ya kunshi ofisohin kafafen yada labarai.
Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra’ila suka yiwa luguden wuta.
Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra’ila suka yiwa luguden wuta. AP – Adel Hana
Kawo yanzu Falasdinawa akalla 69 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da yara 17, yayin da wasu sama da 300 suka jikkata.
Farmakin Isra’ilar dai ya biyo bayan makaman rokar da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harbawa cikin kasar tun a ranar Litinin inda suka halaka mutane 6, bayan karewar wa’adin da Hamas din ta dibarwa Isra’ila kan janye jami’an tsaronta daga Masallacin Al Aqsa, inda suka ci zarafin fararen hula a yayin da suka ibada.
Tashin hankalin baya bayan nan dai ya samo asali ne kan tilasta korar wasu Falasdinawa daga wata unguwa mai suna Shiekh Jarrah, yankin da falasdinawa da Isra’ila suka dade suna shari’a kan hakkin mallakarsa tun shekarar 1972.