London; Jirgin Yan Gudun Hijira Zuwa Rwanda Bai Tashi Kamar Yadda Aka Tsara ba.
An dakatar da tashin jirgin ‘yan gudun hijira na gwamnatin kasar Burtaniya, bayan da tarayyar Turai ta shiga cikin lamarin.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a jiya Talata ce gwamnatin ta bayyana anniyarta na aika tawaga ta farko na yan gudun hijirar zuwa kasar Rwanda bayan da ta sami goyon bayan babban kotun kasar. Amma hakan ya bai faru ba a lokacinda kungiyar tarayyar Turai ta bayyana hakan a matsayin wani abinda bai dace ba.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Burtania ta shirya tsab don maida wasu yan gudun hijira da suka shigo kasar ta barauniyar hanya zuwa kasar Rwanda, amma jim kadan kafin jirgin ya tashi hukuma mai kula da ‘yan gudun hijira ta tarayyar Turai ta gargadi gwamnatin kasar Burtaniya kan yin haka, don bai dace ba. A nan kuma aka dakatar da shirin zuwa sai abinda hali yayi.
Yan siya, malaman addini, da kungiyoyin kare hakkin bil’adama duk sun yi allawadai da shirin gwamnatin kasar ta Burtania na maida wadansu yan gudun hijirar zuwa kasar Rwanda. Kuma a cikin kwanakin da suka gabata ta yi ta kai kawo a gaban kotunan kasar don cimma manufarta amma daga karshe an dakatar da komawar sai abinda hali yayi.