Liz Truss Ta Zama Sabuwar Firaministar Biritaniya A Hukumance.
Sabuwar firaministar Burtaniya Liz Truss ta kama aiki a hukumance kwana daya bayan zabenta a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative.
Tsohuwar ministar harkokin wajen ta Biritaniya, ta gana da Sarauniyar Ingila a fadarta da ke Balmoral Castle da ke Scotland yau Talata a wani bangare na shirye-shiryen rantsar da ita a matsayin firaministar kasar ta gaba.
Wannan na zuwa ne bayan da a safiyar yau din firaminstan mai barin gado Boris Johnson ya gana da Sarauniyar in da ya mika takardar murabus dinsa.
Manyan kalubalen dake gaban sabuwar firaminsitar sun hada da na tattalin arziki a daidai lokacin da matsalar hauhawan farashin kayaki ke dada karuwa a Burtaniya.
READ MORE : Rasha Ta Zargi Amurka Da Hannu Wajen Haifar Da Matsalar Samar Da Gas Ga Kasashen Turai.
Karin dai na da nasaba ne da karuwar farashin makamashi irinsu iskar gas da kuma wutar lantarki dake addabar kasashen turai da dama sakamakon rikicinsu da Rasha kan yakin Ukraine.
READ MORE : IRGC : Iran Ta Zarce Manyan Kasashen Duniya A Fannin Fasahar Tsaron Sararin Samaniya.
READ MORE : Isra’ila Ta Kai Hari Da Makami Mai Linzami A Filin Jirgin Sama Na Aleppo Da Ke Siriya.
READ MORE : Za A Kashe Dala Biliyan 25 Don Yakar Dumamar Yanay.