Liverpool na ci gaba da kokarin tabbatar da burinta na lashe kofuna hudu a kakar wasannin bana bayan da ta samu nasarar doke Villareal da kwallaye 3-2 a zagaye na biyu na fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar zakarun Turai, matakin wasan gab da na karshe.
A jumulce dai, Liverpool ta samu nasara da kwallaye 5-2 idan aka hada lissafin sakamakon wasansu zagayen farko da suka yi a Ingila a makon jiya.
Yanzu haka Liverpool ta samu gurbi kai tsaye a matakin wasan karshe na gasar ta zakarun Turai, kuma a karo na uku kenan cikin shekaru biyar da kocinta Jurgen Kloop ke kai ta wannan matakain.
Liverpool za ta hadu da kodai Real Madrid ko kuma Manchester City a wasan na karshe wanda za a yi a ranar 28 ga watan nan na Mayu a birnin Paris.
Yau ne Real Madrid da Manchester City za su sake haduwa a Santiago Bernabeau domin buga zagaye na biyu.
Kodayake Manchester City na kan gaban Real Madrid da kwallaye 4-3 kawo yanzu.
Tuni kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, dole ne ya dauki kasada a wasan na yau matsawar suna son samun nasara akan Manchester City.
A wani labarin na daban Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce watakila yayi ritaya idan ya bar kungiyar da ta zama zakarar gasar La-Liga a bana, sai dai ya ce a shirye yake ya cigaba da zama tare da Madrid din tsawon shekaru masu yawa a nan gaba.
Ancelotti dan kasar Italiya mai shekaru 62 a duniya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma zai jagoranci karawa da Manchester City ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai.
Yanzu haka dai Kocin dan kasar Italiya yana yarjejeniya da Real Madrid har zuwa shekarar 2024, bayan da ya koma kungiyar a karo na biyu a shekarar bara daga kungiyar Everton.
Yayin wata zantawa da manema labarai ne kuma, Ancelotti ya ce zai iya cigaba da horas da Real Madrid tsawon shekaru 10, idan kungiyar ta bukaci hakan.