Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta shiga jerin manyan kungiyoyin Turai da ke zawarcin dan wasan gaba na Jamus Karim Adeyemi.
Matashin dan wasan mai shekaru 19 wanda ke taka leda da FC Salzburg, Club din da kansa ya sanar da cewa a shirye ya ke ya raba gari da shi a karshen wannan kaka.
Yanzu haka dai kungiyar ta Salzburg ta sanyawa Karim Adeyemi farashin yuro miliyan 25.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar mai doka gasar Firimiya a shirye ta ke ta sayo Adeyemi.
Matashin dan wasan wanda tauraruwarsa ke haskawa zuwa yanzu ya zura kwallaye 8 cikin wasanni 10 da ya doka a wannan kaka.
A awani labarin na daban da yiwuwar babu ko da dan wasan Liverpool daya da zai halarci wasannin Olympic da zai gudana a birnin Tokyo na Japan, wasannin gasar da za su kankama a watan gobe bayanda annobar covid-19 ta tilasta dage gasar daga bara da aka tsara zuwa bana.
Za dai a faro wasannin na Olympics da corona ta hana bara ne a ranar 22 ga watan yuli mai kamawa a kuma karkare a ranar 7 ga watan Agusta.
Duk da sakon na Liverpool shugaban hukumar kwallon kafar Masar Ahmed Mujahed ya bayyana fatan dan wasan ya iya samun alfarmar takawa kasar Leda.
Salah mai shekaru 29 fiye da shekara guda kenan anan dambarwa kan yiwuwar ya rasa damar takawa kasar tasa leda a wasannin na Olympic.
A cewar Mujahed ba ya tilastawa Salah ya takawa Masar leda a wasannin gasar amma abu ne mai matukar wahala ga kasar da shi kansa dan wasan, a iya zuwa gasar ba tare da shi ba.
Baya ga Salah ‘yan wasa irinsu Minamino da Ibrahim Konate dukkaninsu bazasu samu damar dokawa kasashensu wasannin ba.