Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana cewa yanzu ya na da kwarin gwiwar iya lashe kofin firmiyar bana, dai dai lokacin da ya rage wasa 1 tal a kammala gasar ta firimiya amma Manchester City ke jagoranci da maki 1.
A cewar Jurgen Klopp ko shakka babu ba za su karaya ba har sai sun ga abin da hali zai yi, ya na mai cewa za su yi kokarin lashe maki 3 na haduwarsu da Wolverhampton a Anfield ranar 22 ga watan nan dai dai lokacin da Manchester City jagora ke shirin haduwa ta Aston Villa wato tawagar Steven Gerard tsohon zakaran Liverpool.
Liverpool dai ta matsa kaimi ga City fiye da yadda ta yi mata a kakar wasan da ta gabata, ganin yadda har sai a ranar karshe ne za a iya tantance zakarar bana sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya.
Idan har dukkaninsu suka iya nasara a wasan karshen kai tsaye City ta sha da kyar amma idan har ta yi barin maki Liverpool ka iya bayar da mamakin lashe kofin.
Haka zalika idan kungiyoyin biyu suka yi kan kan kan a yawan maki bayan wasan na karshe, kenan Man City za ta iya dage kofin da banbancin yawan kwallaye.
A watan Janairu dai City ta bai wa Liverpool tazarar maki 14 ne amma kuma Reds din ta matsawa tawagar ta Pep Guardiola lamba ta yadda tazararsu ta dawo maki 1 tal a yanzu haka, bayan nasarori 15 canjaras 2 a wasanni 17 da ta doka daga lokacin zuwa yanzu.