Limamin Juma’ah na Tehran Hujjatul-Islam Haj Ali Akbari ya yaba da kalaman shugaban kasar Iran Ayatullah Al-Sayed Ibrahim Raisi a majalisar dinkin duniya, inda yace haƙiƙa shi ne ma’auni na diflomasiyyar Gwagwarmaya, yana mai cewa a wani bangare na karshen hudubarsa kare wurare masu tsarki lamari ne mai girma a tarihin Iran mai juyin juya hali.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, limamin sallar juma’a a birnin Tehran, Hujjatul-Islam wal-Muslimin Muhammad Jawad Haj Ali Akbari a cikin hudubarsa da ta zo daidai da ranar da aka gudanar da Makon tsaro na kariyar kai mai tsarki a hudubar sallar Juma’a a birnin Tehran ya tabo batun jajircewa da dakewar da Iraniwa su ka yi a lokacin yakin, inda ya tabbatar da cewa wancen lokaci shine mafi girma na tsaron mutane yana da wata fa’ida ta musamman ta zamantakewa da kuma wani matsayi a tarihin al’ummar Iran.
Kuma a cewar Hujjatul-Islam Ali Akbari, lokacin kariya mai tsarki a lokacin yakin da aka dorawa Iran (1980-1988) shi ne hadin kan al’ummar Iran muminai masu juyin juya hali, kuma ana daukar wannan rana a matsayin ranar tarihi a cikin juyin juya halin Musulunci na tarihin al’ummar Iran masu juyin juya hali inda al’ummar Iran suka sami damar kare kansu karkashin jagorancin Imam Al-Khumaini (RA) a tsawon shekaru takwas, lamarin ya kasance wani sauyi a tarihin Iran da yankin da kuma duniya baki daya.
Dangane da faretin sojoji da aka gudanar a yau a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan makon tsaro mai tsarki, mai wa’azin na Juma’a ya ce hakan shi ne ya nuna ma’aunin gwagwarmaya.
Hujjatul-Islam Haj Ali Akbari ya yi ishara da tafiya da shugaban kasar Iran ya yi zuwa birnin New York domin halartar taron majalisar dinkin duniya, a matsayin misali mai kyau na samun nasarar diflomasiyya gwagwarmaya.
Hujjatul-Islam Akbari ya kara da cewa shugaban kasar Iran ya gabatar da jawabi a wajen taron da ya wakilci al’ummar Iran a gaban dukkan Al’ummun duniya da kuma kafafen yada labarai na kasashen duniya daban-daban, kuma ya kasance mai magana da yawun wadanda ake zalunta a duniya na shahidai, da ‘ya’yan al’ummar Iran, ya kuma kara shelar mutuwa ga girman kai, ya kuma bitar abubuwan da ke faruwa a duniya ta hanya mai kyau.
Dangane da batun cin mutuncin kur’ani mai tsarki, limamin Juma’ar na Tehran ya bayyana cewa: Shugaban kasar a yayin jawabinsa ya daga kwafin kur’ani mai tsarki, inda yayi Alla wadai da tozarta Alkur’ani tare da nuna goyan bayansa na kariya gareshi wanda hakan ke nuni abu mai muhimmnaci wajen kariya ga Alkur’ani mai tsarki.
Hujjatul-Islam Haj Ali Akbari ya kara da cewa jawabin shugaba Ibrahim Raisi wani tsarin diflomasiyya ne da ya ginu bisa gwagwarmaya, al’adun kare wuri mai tsarki da juyin juya halin Musulunci, wanda ya taimaka wajen fitar da kadarorin Iran, nesa ba kusa ba na diflomasiyya na bara. tare da tabbatar da cewa diflomasiyyar gwagwarmaya ota ce tayi sanadiyyar sakin fursunonin da kuma korar da Yahudawan sahyoniyawa daga cikin taron majalissar dinkin Duniya.
Source: LEADERSHIPHAUSA