Duk da cewa annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a fadin duniya, wasu likitocin da kasar Sin ta turawa kasashen waje domin ba da tallafi suna ci gaba da gudanar da aikinsu na ceton rayukan jama’a a sassa daban daban na fadin duniya.
Jiang Jiarui, wanda ya taba aiki a asibitin cutar kansa na lardin Hunan na kasar Sin, daya ne daga cikin tawagar ma’aikatan kiwon lafiya da kasar Sin ta turawa Zimbabwe, inda yanzu yake aiki a asibitin Parirenyatwa dake kasar. Ya kuma shaida mana cewa, “Ana kiran likitocin da ake turawa ketare domin ba da tallafi, da sunan jami’an diplomasiyya masu sa kayan likita, gaskiya ne muna gudanar da aiki a madadin kasarmu.”
Yanzu haka suna fuskantar matsaloli daban daban sakamakon yaduwar annobar COVID-19, amma Jiang Jiarui ya bayyana cewa, zai ci gaba da aiki a kasar ta Zimbabwe, ta yadda zai kammala aikin ba da tallafin kiwon lafiya a ketare, da kasarsa ta ba shi.
A wani labarin na daban katafaren yankin raya masana’antun fasahohin zamani na Zhongguancun, da ake wa lakabi da “Silicon Valley” na kasar Sin, ya samu karin kaso 27.8 kan kudin shigarasa a watanni 8 na farkon bana, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
A cewar hukumar, kamfanonin bangarorin fasahar sadarwa da laturoni, da fannin injiniya mai nasaba da halittu da sabbin fasahohin kiwon lafiya, sun samu dorewar ci gaba
Adadin ma’aikata a fannin bincike da kirkire-kirkiren fasaha a kamfanoni dake yankin Zhongguancun, ya kai 751,000 a wancan lokaci, adadin da ya karu da kaso 8.9 akan na makamancin lokacin a bara.
Zhongguancun da aka kafa a shekarar 1988 a arewa maso yammacin birnin Beijing, wanda ya kunshi jami’o’i da cibiyoyin bincike, shi ne yankin raya masana’atun fasahohin zamani na farko a kasar Sin.