Libya; Bangarorin Da Ke Rikici Na Zargin Juna Da Tayar Da Rikici A Tripoli.
Gwamnatin hadin kan kasa ta Libya karkashin jagorancin Abdel Hamid al-Dabaiba ta zargi magoya bayan Fathi Bashagha, shugaban gwamnatin da majalisar wakilai ta nada, da kawo cikas ga tattaunawar da aka yi domin ganin an ceto birnin Tripoli daga wani sabon tashin hankali.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin Dabaiba ta fitar a jiya Asabar, ta ce fadan da ya barke a babban birnin Tripoli , ya biyo bayan tattaunawar da ake yi na ganin an kawar da zubar da jinin babban birnin kasar ne, tare da aiwatar wani shiri wanda ya tilastawa dukkanin jam’iyyu gudanar da zabe a karshen shekara, a matsayin mafita ga rikicin siyasar kasa.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a gaggauta dakatar da bude wuta a kasar ta Libya bayan da aka kwashe kwana guda ana ta mummunar arangama tsakanin bangarorin ‘yan siyasa a birnin Tripoli.
READ MORE : Iran; Hulda Da Afirca Na Daya Daga Cikin Manufofin Siyasarmu.
Tun bayan kisan gillar da ‘yan bindiga tare da taimakon kasashen NATO suka yi wa tsohon jagowan kasar Libya marigayi Kanal Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekara ta 2011, har inda yau take kasar bat a sake sheda zaman lafiya ba.