An shiga rana ta 4 a jere da fara taron masu ruwa da tsaki don fasalta kundin tsarin mulkin kasar Libya da Masar ke jagoranta a birnin Cairo, a wani yunkuri na ganin an gudanar da zaben kasar da ta shafe shekaru ta na fama da rikici.
Shiga tsakanin na Masar bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da aka faro a Lahadin da ta gabata, shi ne karo na 3 da ake gudanarwa a kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar da kuma gudanar da zabe.
Ana saran a shafe fiye da mako guda ana zaman tattaunawar wanda zai bayar da damar bibiyar kundin tsarin mulkin kasar ta libya da zai bayar da damar gudanar da zabe a kasar.
Taron ya kunshi mambobin majalisar Libya, da na babban kotun kasar da kuma bangarorin masu bayar da shawarwari baya ga kwararru daga bangarorin siyasa dukkaninsu bisa sanya idanun Majalisar Dinkin Duniya.
Babbar jami’Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan rikicin na Libya ya roki bangarorin da ke cikin tattaunawar su samar da gamsasshiyar matsaya da za ta kawo karshen rikicin siyasar kasar.
A wani labarin na daban wata kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin rai da rai akan shugaban Yan Tawayen Casamance Cesar Atoute Badiate saboda samun sa da laifin kisa bayan ya kaddamar da boren da yayi sanadiyar mutuwar mutane 14.
Lauyan sa Cire Cledor ya kuma ce bayan Cesar an kuma daure wasu mutane biyu da suka hada da Omar Ampoi Bodian da dam jarida Rene Capain Bassene rai da rai a kotun dake Ziguinchor.
A cikin watan Maris na shekarar 2022,Rundunar sojin kasar Senegal ta kaddamar da farmaki kan mayakan da ke kawance da mayakan ‘yan tawayen ‘Casamance’, wata kungiyar ‘yan aware a yankin kudancin kasar.
A ranar 13 ga watan na Maris, sojojin kasar na Senegal suka kaddamar da farmakin kan mayakan ‘yan awaren na Casamance da ake kira da MFDC a takaice, wadanda suke karkashin jagorancin Salif Sadio.
Tun a shekarar 1982 mayakan ‘yan awaren na Senegal suka fara fafutukar yaki da gwamnatin Senegal, bisa zargin gwamnatin kasar da mayar da su saniyar ware.
Mutane 16 ne aka tuhuma da laifin kashe mutane 14 da suka je daji omin neman itace a Bayotte dake kusa da Ziguinchor ranar 6 g awatan Janairun shekarar 2018.