Libya; AN Yi Musayar Wuta Tsakanin Magoya Bayan Yan Siyasa A Kasar.
An samu bullar dauki ba dadi tsakanin bangarori biyu masu dauke da makamai a tsakiyar birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya.
A cikin daren jiya Juma’a wayewar garin yau Asabar bangarori biyu masu dauke da makamai a birnin Tripoli sun yi musayar wuta lamarin day a janyo tashin hankali da firgita a tsakanin al’ummar birnin.
Rahotonni sun bayyana cewa; Dauki ba dadin ya kunno kai ne tsakanin bataliyar Annawasiy da rundunar sa-kai da take taimakon wanzar da zaman lafiya a birnin na Tripoli, inda bangarorin biyu suka yi amfani da manyan makamai da matsakaita da kuma kanana wajen neman yin galaba a kan junansu.
READ MORE : Ba’amurke mai fallasa; An kashe mai safarar mutane kuma abokin Trump a kurkuku.
Wannan tarzoma tana zuwa ne a daidai da aka samu rabuwan kai tsakanin jami’an kasar inda ake da gwamnatoci biyu a kasar tsakanin gwamnatin hadin kan kasa da ke birnin Tripoli karkashin Abdul-Hamid Addabaiba da ta Fatahi Bashagha da ked a matsuguni garin Tabruk a shiyar gabashin kasar da Majalisar Dokokin Kasar ta amince da shi.