Birnin Benghazi na kasar Libya ya fuskanci girgizar kasa mai karfin awo 5.9 a ma’aunin Richter da ta dauki tsawon dakikoki da dama a daren jiya Juma’a.
Mazauna birnin sun bayyana a shafukan sada zumunta cewa sun ji girgizar kasar da misalin karfe 11:31 na daren jiya.
Cibiyar nazarin girgizar kasa ta Euro-Mediterranean ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa, an ji girgizar kasar a cikin teun Mediterrenean mai tazarar kilomita 189 daga arewa maso yammacin birnin Benghazi na kasar Libya.
Cibiyar ta yi nuni da cewa girgizar ta kasance mai karfin awo 5.9 a ma’aunin Richter, kuma a zurfin kilomita 10 a karkashin kasa.
A karon farko tun bayan rikicin Rasha da Ukraine, wani jirgin ruwa ya tunkari kasar Ukraine domin dibar tsaba zuwa nahiyar AFrika.
An bayyana jirgin ruwan zai nufi kasar Habasha a karkashin wani shiri da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya na fitar da hatsi daga Ukraine domin shawo kan matsalar abinci a duniya.
Rikicn Rasha da Ukraine manyan kasashe wajen samar da alkama ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo a duniya tare da haifar da matsalar karancin abinci a kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da kuma wasu sassan Asiya.
A wani labarin na daban a karon farko a cikin ‘yan kwanakin nan, jiragen ruwa da yawa masu jigilar hatsi sun bar tashoshin jiragen ruwa na Ukraine a karkashin sabuwar yarjejeniyar, amma yawancin jigilar kayayyaki abinci ne na dabbobi.
A ranar Juma’a, shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za a yi lodin kayan agaji na farko da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya zuwa Afirka, kuma hatsin da za’a kai kasar Habasha, na daga cikinsu.
A karon farko jirgin mai suna Brave Commander, ana sa ran zai dauki fiye da ton 23,000, a cewar ma’aikatar samar da ababen more rayuwa ta kasar Ukraine.
Habasha, tare da Somaliya da ke makwabtaka da Kenya, na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru arba’in a yankin kahon Afrika.
Source: ABNA