Libiya; Wani Rikici Ya Yi Ajalin Mutum 23.
Rahotanni daga Libiya na cewa kura ta lafa a Tripoli babban birnin kasar bayan wani fada da ya barke tsakanin gungun masu dauke da makamai a yammacin birnin.
Akalla mutum 23 ne suka mutu kana wasu kimanin 140 suka jikkata a rikicin, a cewar hukumomin kiwon lafiya na kasar.
Fadan da ya barke a cikin daren Juma’a zuwa Asabar, tsakanin gungun dake gaba da juna ya faru ne a cikin unguwanni da dama dake yammacin Tripoli, inda akayi ta ji karar fashewa da kuma aman wuta.
An samu barna mai yawa a cewar wani dan jarida an kamfanin dilancin labaren AFP, inda motoci da gidaje da dama suka kone.
Labarin bai ambato musababin barkewar fadan ba, amma an rawaito gwamnatin Tripoli na zargin firaminista Fathi Bachagha, dake Syrte a tsakiyar kasar mai samun goyan bayan Marshal Khalifa Haftar, da yunkurin kwace birnin.
Tun dai bayan da majalisa ta nada shi, M. Bachagha, ke yunkuri tare da barazanar ganin ya shiga birnin domin tabbatar da ikonsa.
Shi kuwa Abdelhamid Dbeibah, dake jagorantar gwamnatin wucin gadi, ya fake da cewa ba zai mika mulki ba illah ga gwamnatin da aka zama ta hanyar kada kuri’a.