Libiya; Dakarun Haftar, Sun Janye Daga Kwamitin Yarjejeniyar Berlin.
A Libiya, dakarun dake biyaya ga Khalifa Haftar, mai karfin fada aji a gabashin kasar, sun sanar da janyewa daga kwamitin 5+5 na yarjejeniyar siyasar da aka cimma a tattaunawar Berlin, kamar yadda suka sanar a wani bidiyo.
A cikin sanarwar sojojin sun bukaci Janar Khaftar din, da ya toshe hanyoyin cibiyoyin man fetur, da hanyoyin da suka hada gabashi da yammacin kasar, da kuma dakatar da sufirin jiragen sama tsakanin yankunan na gabashi da yammaci da kuma dakatar da duk wata irin alaka da gwamnatin Abdul Hamid Dbeibah, wanda suka dorawa alhakin rashin samun albashinsu na tsawon watanni hudu.
Gwamnatin Tripoli dai ta bukaci a bata dukkan sunaye da kuma matsayi na dakarun na ANL, domin biyansu albashi, saidia Benghazi ta ce ba zatayi hakan ba saboda dalilai na tsaro..
Yarjejeniyar da aka cimma a 2020 ta tanadi batutuwa da dama da suka shafi siyasa da kuma tattaunawra da ta kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
READ MORE : Guterres Ya Damu Game Da Ruruwar Wutar Rikici Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila.
An bayyana Janyewar dakarun daga kwamitin da babban koma baya tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma shekaru biyu da suka gabata.