Lebanon ta yi gargadin cewa yaki zai iya barkewa a yankin saboda abin da Isra’ila ke yi
Hare-haren da Isra’ila ta kwashe kwana 83 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 21,110, ciki har da yara 8,800 da mata 6,300, sannan sun jikkata fiye da mutum 55,243.
Firaministan kasar Labanon Najib Mikati, ya yi gargadin cewa za a yi yaki mai cike da rudani a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda tsokanar Isra’ila.
1648 GMT — Labanon ta yi gargadin cewa yaki zai iya barkewa a yankin saboda abin da Isra’ila ke yi
Firaministan kasar Labanon Najib Mikati, ya yi gargadin cewa za a yi yaki mai cike da rudani a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda tsokanar Isra’ila.
Sanarwar da majalisar ministocin kasar ta fitar ta ambato Mikati yana fada a yayin ganawarsa da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron a Beirut cewa, “Ci gaba da tsokanar da Isra’ila ke yi a kudancin Labanon na iya haifar da tabarbarewar al’amura da kuma barkewar yakin basasa a yankin.”
“Kofar dakatar da yakin Gaza ta fara ne da tsagaita wuta, sannan kuma a ci gaba da yin shawarwari kan yadda za a cimma matsaya kan tsarin kasashe biyu da bai wa Falasdinawa ‘yancinsu,” in ji Mikati.
1313 GMT — Masar na jiran martani kan shirin kawo karshen zubar da jini a Gaza: Alkahira
Masar ta tabbatar da cewa ta gabatar da wani tsari na kawo karshen yakin da Isra’ila ke yi a Gaza wanda ya ƙunshi matakai uku da za su kawo tsagaita wuta, ta kuma ce tana jiran martani kan shirin.
Shugabar Hukumar Yada Labarai ta Masar din, Diaa Rashwan, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce Masar za ta ba da cikakkun bayanai kan shirin da zarar an samu wadannan martani.
Shawarar wani yunƙuri ne na “na kusantar da ra’ayi tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa, don dakatar da zubar da jinin Falasɗinawa da cin zarafi a kan Gaza da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” in ji shi.
Source: IQNAHAUSA