Lebanon Ta nisanta yiwuwar bullar yaki tsakaninta Da Isra’ila kan Rikicin kan iyaka.
Ministan harkokin wajen kasar Lebanon ya nisanta yiwuwar bullar yaki tsakanin Lebanon da Haramtacciyar kasar Isra’ila kan riikicin kan iyaka da ta kunno kai.
Kafin gudanar da zaman tattaunawa tsakaninsa da wakilin kasar Amurka mai shiga tsakani kan sabuwar dambaruwar siyasar da ta kunno kai kan rikicin kan iyaka tsakanin kasar Lebonon da Haramtacciyar kasar Isra’ila; Ministan harkokin kasar Lebanon Abdallah Bou Habib ya tabbatar wa ‘yan kasarsa cewa; Kada su damu saboda matsalar kan iyaka da ta kunnokai a halin yanzu tsakanin Lebanon da Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta kai ga barkewar yaki tsakaninsu ba.
A ganawarsa da manema labarai a yau Talata; Abdallah Bou Habib ya yi furuci da cewa: Babu wata alama daga tsakanin Kungiyar Hizbullah ta Lebanon da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da take nuna yiwuwar ballar yaki a tsakaninsu, duk da cacar baki tsakanin bangarorin biyu bisa dogaro da ingantattun bayanai daga sassa daban-daban da suka dace a aminta das u.
Wakilin kasar ta Amurka mai shiga tsakani ya bayyana fatarsa mai daukeda kwarin gwiwar cewa: Akwai yiwuwar cimma matsaya daya a tattaunawar da ake yi tsakanin Lebanon da Haramtacciyar kasar Isra’ila.