Lebanon; Mutanen Kasar Sun Yi Zanga-Zangar Yin Allawadai da Kokarin Isra’ila Na Satar Man Kasar.
Daruruwan mutane a kudancin kasar Lebanon suka gudanar da zanga-zangar yin allawadai da kokarin hakar iskar gas ko man fetur a yankin Karish na cikin ruwa mallakin kasar, kuma kuma wanda suke da kaddama da HKI kansa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata ne, wani jirgin ruwan hakar iskar gas ko man fetur na kasar Girka ya isa yankin Karis cikin ruwan Medeteranina don fara aikin haka a yankin.
Firas Hamdan, wani dan majalisar dokokin kasar ta Lebanon wanda ya halarci taron gangamin yay i magana a madadin sauran majalisa 13 da suka halarci ganganin, inda yake cewa, bamu amince da barin dukiyar kasar Lebanon ga wanda mallakin duk mutanen kasar ne ga haramtacciyar kasar Isra’ila.
READ MORE : Wasu Kungiyoyi A Sudan Sun Ki Halattar Zaman Sulhuntawa.
Shugaban kasar Lebanon da firai ministan kasar duk sun yi allawadai da kokarin HKI na hakar iskar gas a yankin Karis na tekun Medeteranian, kuma suna ganin hakan wata tsokana ce. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon y ace zata iya hana HKI hakar iskar gas a wannan wurin, amma sai gwamnatin kasar Lebanon ta Amince.