Lebanon; Kungiyar Hizbullah Ta Ce A Shirye Take Ta Hana Isra’ila Hakar Gas A Cikin Teku Kusa Da Kasar.
Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar a shirye take ta hana haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) hakar Iskar gas a yankin Tekun da ake takaddama da ita da kasar Lebanon kan mallakarsa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sheikh Naeem Qasim yana fadar haka a baya da wasu kafafen yada labarai a kasar sun nakalto jami’an gwamnatin kasar na cewa gwamnatin HKI ta kai jirgin ruwa mai hakar iskar gas a yankin tekun mederenina wanda take ta kaddama da gwamnatin kasar Lebanon kan mallakarsa.
Sheikh Naeem Qasim ya kara da cewa a duk lokacinda gwamnatin kasar Lebanon ta tabbatar da cewa HKI ta keta hurumin ruwan tekun kasar kungiyar Hizbullah zata dauki mataki a kan HKI don hanata hakar iskar gas a yankin.
Sheikh Qasim ya kara da cewa dole gwamnatin kasar Lebanon ta dauki matakan da suka dace, idan har tattuanawa kan mallakin yankin ta hannun Amurka ya kasa bada sakamakon da ake bukata. Musamman ganin yadda kasar Lebanon take bukatar arzikinta na cikin tekun medeteranina.
Shugaban kasar ta Lebanon Michel Aun ,da Firai ministan kasar Najib Mikata da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Berri duk sun gargadi HKI kan hakar man fetur ko iskar gas a wannan yankin.