Lebanon; Jami’an Tsaron Isra’ila Suna Shirin Fuskantar Barazar Hizbullah.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana fara shirin fuskantar barazanar da kungiyar hizbullah ta yi na tarwatsa rijiyoyin hakar mai da iskar gas na kasar matukan ba’a cimma yarjeniya da gwamnatin kasar Lebanin a karshen wannan watan nan ba kan shata kan iyakar kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wasu majiyoyin Haramtacciyar kasar na cewa saboda tsoron barazanar da shugaban kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasarallah ya yi a cikin yan makonnin da suka gabata dangane da takaddamar shata kan iyakar ruwa ta Karish tsakanin Lebanon da HKI, sun fara daukar matakan ganin an rage asararo ko da barazanar ta tabbata.
READ MORE : Iran Ta Bukaci Kasar Sweden Ta Mutunda Hakin Dan Kasar Wanda Aka Daure Bisa Zalunci.
A wani bangare kuma shugaban kungioyar Hizbullah ya fadawa gwamnatin Lebanon kan cewa kada ta yarda ta saryar da hakkin mutanen kasar Lebanon a yankin ruwa na Karish. Sayyid Nasarallah ya ce mai shiga tsakani HKI da Lebanon, baamerike yana bata lokaci ne kawai, don damar da aka baci ya rika ya wuce.
READ MORE : An Bude Taron Tattaunawa Na Kasa A Birnin N’Djamena Na Kasar Chadi.