Lebanon; Hizbullah Ta Ce Samar Da Huldar Jakadanci Tsakanin Saudiya Da Isra’ila Barazana Ce Ga Lebanon.
Wani babban jami’a a kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa samar da huldar jakadanci tsakanin kasar Saudiya da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) barazana ne kai tsaye ga kasar Lebanon.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheikh Nabil Qawoos mataimakin shugaban majalisar koli ta kungiyar yana fadarb haka a jiya Litinin a wani taro a garin Bint Jbel na kudancin kasar.
Qawoos ya kara da cewa HKI zata yi amfani da kasar Saudia don kutsawa cikin kasashen da suke gwagwarmaya da ita, musamman kasashen Siriya Lebanon da Falasdinu da ta mamaye.
Kafin haka ministan harkokin wajen HKI Yair Lapid ya bayyana a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata, kan cewa, tare da taimakon Amurka da kuma wasu kasashen larabawa gwamnatinsa tana kokarin samar da huldar jakadanci mai karfi tsakaninta da kasar Saudiya. Kuma y ace yana fatan nan ba da dadewa ba wannan manufar zata tabbata.
Kafin haka dai HKI tare da taimakon gwamnatin Amurka ta samar da huldar jakadanci da kasashen larabawa, wadanda suka hada da UAE, Bahrain, Sudan Morocco. Sannan dama ta dade tana da wannan huldar da kasashen Masar da Jordan.