Lebanon; Hizbullah A Shirye Take Ta Kare Dukiyar Kasar Da Ke Cikin Ruwan Kasar.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kungiyarsa a shirye take ta kare duniyar kasar dake cikin ruwan tekun Mederenian, sannan dukkan zabi na hannunta.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyid Hassan Nasarallah yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a talabijin ta Almanar da Almayadeen na kasar Ta Lebanon a jiya da yamma.
Nasaralla ya kara da cewa kungiyarsa tana da hanyoyi da dama wajen hana HKI hakar iskar gas a yankin da take takadda da kasar Lebanon kan mallakarsa. Banda haka ya ja kunnen kamfanin hakar kasar ta kasar Girka wanda ya isa yankin Karshi da aka takaddama a kansa kan cewa duk abinda ya faru da jirgin ruwan hakar gas dinta ita ta jawo.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin da kuma mutanen kasar Lebanon kan su gaggauta fara hakar Iskar gas da man fetur da suke wadannan yankunan na ruwan kasar Lebanon don sune kadai mafita wa mummunan halin tattalin arzikin da kasar take fama da shi a halin yanzu.
Shugaban kungiyar ya maida martani ga HKI kan cewa barnan da zata yiwa yahudawan a duk wani yakin da zai barke a tsakaninsu nan gaba sai yafi wanda zata yiwa Lebanon.
A makon da ya gabata ne aka ga jirgin hakar gas ta HKI ta zo kan yankin da ake takaddama da kasar Lebanon kan mallakarsa da nufin fara hakar Gas a yankin.