Lebanon Gwamnatin Kasar Ta Bukaci MDD Ta Takurawa Isra’ila Ta Daina Keta Sararin Samaniyar Kasar.
Sojojin kasar Lebanon sun bukaci MDD ta takurawa haramtacciyar kasar Isra’ila, don ta daina keta sararin samaniyar kasar, saboda kai hare-hare kan makobciyar, kasar Siriya, da kuma keta hurumin kasar ta sama kasa da ruwa da take yi a duk sanda ta ga dama.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tawagar sojojin kasar ta Lebanon karkashin jagorancin Burgediya Janar Haseeb Abdo ne ta gana da kwamandan dakarun MDD a kasar Lebanon UNIFIL Manjo Janar Stefano Del Col a garin Ras Naqoura na kudancin kasar Lebanon a jiya jumma’a.
Sojojin kasar ta Lebanon sun bukaci Majalisar ta hana HKI keta sararin samaniyar kasar, idan kuma ta kasa yin haka, sojojin kasar zasu dauka matakan da suka dace wand aba zai yiwa wadanda abin ya shafa dadi ba.
Rundunar UNIFEL da MDD dai ta dade a kudancin kasar Lebanon da sunan tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasar ta HKI amma bata aikinta kamar yadda ya dace.