Lebanon; A Karo Na Bakwai An Zabi Nabih Berri A Matsayin Shugaban Majalisar Dokoki.
Sabuwar majalisar dokokin Lebanon ta sake zaben Nabih Berri a matsayin shugaban majalisar a karo na bakwai kuma shekara 30 a jere.
Sabuwar majalisar wakilai ta sake zaben kakakin majalisar Nabih Berri a matsayin shugaban majalisar a karo na bakwai, da kuri’u 65 ba tare da jayayya ba, yayin da kuma aka jefa wasu kuri’u 23 da babu rubutu a kansu.
Bayan zabensa, shugaban majalisar Nabih Berri ya bayyana cewa, zai yi aiki tare da dukkanin bangarori, domin kuwa yana wakiltr dukkanin al’ummar Lebanon ne ba tare da wani banbanci ba.
Berri ya ce, akwai bukatar hada karfi da karfe wajen yin watsi da duk wani sabani, sannan kuma ya kamata a kawo karshen duk wani batu na kulla alaka tsakanin Lebanon da Isra’ila.
An kuma zabi Elias Bou Saab mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon da kuri’u 65.
Shi ma dan majalisar Alain Aoun ya samu mukamin Sakatare, wanda aka saba nadawa ga daya daga cikin ‘yan majalisa kiristocin Maronites a zauren majalisar.
Nabih Berri dai shi ne shugaban kungiyar Amal wadda take yaki da isra’ila tare da kungiyar Hizbullah, kamar yadda kuma suke da hadin gwiwa wajen daukar matsaya ta siyasa.