Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar takararsa Marine Le Pen sun yi musayar zafafan kalamai a yau Litinin, a dadai lokacin da suke komawa fagen yakin neman zabe gabanin fafatawarsu a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.
‘Yan takarar biyu sun gudanar da kwarya-kwaryar gangami a yayin bikin Easter, suna rige-rigen tallata kansu gabanin muhawararsu ta keke da keke da za su yi a ranar Laraba mai zuwa.
A yayin wannan muhawara, ana sa ran shugaba Emmanuel Macron mai ra’ayin ‘yan tsaka-tsaki ya kare salon mulkinsa na tsawon shekaru biyar a gaban Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi.
Tarihi zai maimata kansa a bana, ganin cewa a shekara ta 2017, shugaba Macron ne da Le Pen suka fafata da juna a zagaye na biyu na zaben a wancan lokaci.
A karo na uku kenan da Le Pen ke neman darewa kujerar shugabancin Faransa, yayin da a bana take jaddada cewa, tana cikin kyakkyawan shiri fiye da sauran lokuta a baya.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, shugaba Macron na kan gaba a yiwuwar samun nasara a zaben fiye da Le Pen.
A wani labarin na daban Gwamnatin mulkin sojin da ta karbe mulki a kasar Guinea da ke yammacin Afirka ta kaddamar da wani “daftari” da ta ce za ta yi amfani da shi wajen mayar da mulkin kasar ga farar hula.
In ba a mance ba, a ranar 5 ga watan Satumba ne dakarun da ke karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumbouya suka kama shugaba Alpha Conde mai shekaru 83 a duniya, bayn sun sun kifar da gwamnatin sa.
Yayin da Jakadan kasar Guinea a Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa taron Majalisar cewa, za a gudanar da gyare gyare kan kundin zaben kasar tare da rubuta sabon kundin tsarin mulki gabanin sabon zaben.
majalisar mai da mulki ga farar hular ta CNT mai kunshe da mambobi 81 da aka zabo daga jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin kwadago, masu daukar ma’aikata, jami’an tsaro da sauran hukumomi, za a dorawa alhakin tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar.