Lavrov; Kasashen Yammacin Duniya Na Adawa Da Ci Gaban Afirka.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana a yau Laraba cewa, kasashen Afirka na kokarin fayyace makomarsu da kuma warware matsalolinsu, lamarin da ya ce kasashen yammacin duniya ke adawa da shi wajen neman mulkin Amurka.
Lavrov ya kai ziyara birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda ya kammala rangadin kasashen Afirka hudu, a daidai lokacin da Moscow ke fafatawa da kasashen yammacin duniya kan rikicin sojan Rasha da Ukraine.
Babban jami’in diflomasiyyar na Rasha ya kuma ce Moscow na goyon bayan yunkurin Habasha na daidaita al’amuran siyasarta na cikin gida, wanda ya ce ya saba da tsoma bakin kasashen yamma.
“Mun tabbatar da goyon bayanmu ga kokarin da gwamnati ke yi na daidaita al’amura da kuma kaddamar da tattaunawa ta kasa da kasa domin warware muhimman tambayoyi,” in ji Lavrov yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Habasha Demeke Mekonnen.
Demeke ya ce kasarsa na godiya da irin goyon bayan da Rasha ke ba mu wajen kare martabar kasar Habasha.
Gwamnatin Habasha ta zargi masu sukanta na kasashen waje da neman yin katsalandan ba bisa ka’ida ba a cikin harkokin cikin gidanta.
Tuni Lavrov ya ziyarci Masar da Jamhuriyar Congo da kuma Uganda.
Yayin ganawarsa da Lavrov a ranar Talata, shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce bai ga dalilin sukar Rasha kan rikicin sojan da ta ke yi da Ukraine ba, yana mai jinjinawa abokantakar Rasha da Afirka.
Lavrov ya yaba da abin da ya bayyana a matsayin “madaidaicin matsayi da Uganda da sauran kasashen Afirka suka dauka”, yana mai cewa kasashen yammacin duniya na nuna ra’ayin ‘yan mulkin mallaka ta hanyar neman Afirka ta dauki matakin kin jinin Rasha.