Lauyoyin Assange Sun Kai Karar CIA Kan Yi Musu Leken Asiri.
Wasu gungun ‘yan jarida da lauyoyi sun shigar da karar hukumar leken asirin Amurka CIA da tsohon daraktanta Mike Pompeo, inda suka ce hukumar ta yi musu leken asiri a lokacin da suka ziyarci wanda ya kirkiro shafin na Wikileaks Julian Assange a zamansa a ofishin jakadancin Ecuador da ke Landan.
Shari’ar da aka shigar a ranar Litinin, ta ce a karkashin Pompeo, CIA ta keta hakkokin ‘yan jarida da lauyoyin Amurkawa ta hanyar leken asiri.
READ MORE : Vieira; Akwai Bukatar Kara Zage Dantse Domin Yaki da Wariyar Launin Fata.
Hukumar ta CIA, wacce ta ki cewa komai kan karar, an hana ta tattara bayanan sirri kan ‘yan kasar Amurka. Sai dai kuma wasu ‘yan majalisar sun yi zargin cewa hukumar na da ajiyar bayanan sadarwar Amurkawa a asirce.
READ MORE : Kungiyar EU Tana Nazari Kan Martanin Iran Game Da Batun Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya.
READ MORE : Wang Wenbin: Bayanan Kirkira Na Kafafen Yada Labaran Birtaniya Game Da Chaina.
READ MORE : Rasha Ta Kuduri Aniyar Kara Fadada Alakarta Da Koriya Ta Arewa A Dukkanin Bangarori.
READ MORE : Mali; Masu Zanga-Zanga Sun Bai Wa Sojojin Faransa Na “Barkhan” Sa’o’i 72 Da Su Fice.