Mahukuntan Isra’ila na da alhakin “Laifukan yaki kan bil’adama” da suka aikata a lokacin yaƙin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoban 2023, in ji wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.
Kwamitin Bincike na Kasa da Kasa na Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewar mahukuntan Isra’ila na da alhakin “laifukan yaki na yunwatarwa a matsayin makami da kisan jama’a da gangan da raba mutane da matsugunansu ta karfi da fyade da cutarwa da muzantawa mai tsanani da tsare jama’a ba gaira babu dalili da keta mutuncin dan’adam.”
Kwamitin ya gano cewa an aikata laifukan yaki da suka hada da “cin zarafin bil’adama da kashe rayuka da dama da zaluntar maza manya da yara kanana Falasdinawa da kisan kai da raba mutane da matsugunansu da cutarwar keta haddi” a Gaza.
Kisa da jikkata fararen hula a Gaza da rushe gine-ginen fararen hula a Gaza, sun faru ne saboda shirin aikata hakan da nufin cutarwa mafi muni, an yi watsi da ka’idojin rabe aya da tsakuwa da bambancewa da daukar matakan kula.”
Rahoton ya kara da cewa “Amfani da munanan makamai manya da ke iya yin barna a yankuna da gangan ya zama “harin ganganci kuma na kai tsaye a kan fararen hula.”
Game da kalaman da mahukuntan Isra’ila suka yi, rahoton ya ce kalaman nasu “sun zama na zuga da tayar da rikici kuma na iya zama wasu laifuka na kasa da kasa,” yana mai karawa da cewar ingiza kisan kiyashi babban laifi ne a karkashin dokokin kasa da kasa.
Kwamitin ya kuma auna umarnin kwashe mutane da Isra’ila ta bayar da cewa “ba su isa ba, kuma umarnin na da matsala da rikitarwa, sannan ba su bayar da isasshen lokaci ga jama’a na su bar yankunan ba.”
“Dadin dadawa, hanyoyin fitar jama’a da kwashe su da aka ce suna da tsaro, sun fuskanci hare-haren sojojin Isra’ila,” in ji kwamitin. “Dukkan wannan, ya zama tirsasawa su bar gidajensu.”
Isra’ila ta kuma ‘mamayi’ Gaza wadda “ukuba ce ga al’umma baki daya” wanda ya keta haddin fararen hula, in ji rahoton na MDD.
“Mahukuntan Isra’ila sun aike da makamai ga mayakansu a yankunan da suka yi wa kawanya, kuma run yi amfani da kayan da ke kubutar da rayuwa kamar ruwan sha da abinci da lantarki da man fetur da taimakon jinkai, a matsayin dabarun yaki da karfin ikon siyasa.”
Kwamitin ya kuma jaddada cewar mamayar ta “yi tasiri kan kowa” ciki har da mata masu juna biyu da nakasassu, da kuma raunata yara kanana da suke kamuwa da cututtukan da ke da alaka da yunwar da rashin abinci ta jawo.”
Game da abubuwan da ake yi a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, kwamitin ya gano cewa Isra’ila ta aikata “fyade da cutarwa da muzanta wa dan’adam da ukuba marar dadi, wadanda dukkan su laifukan yaki ne.”
DUBA NAN: Ministan Harkokin Yakin Isra’ila Ya Sauka Daga Mukamin Sa
Haka kuma, kwamitin na MDD ya kaddara cewar gwamnatin Isra’ila tare da rundunar sojin kasar, “sun bayar da izini da bayar da dama da taimakawa ingiza” yakar falasdinawa a Yammacin gabar Kogin Jordan.