Kamar yadda labarai suke shigo mana sun tabbatar da cewa dukkan shirye shirye sun kammala domin gabatar da wannan babbar ibada mai dimbin falala ta tattakin Imam Hussain (S.a) a birnin karbala dake kasar Iraki.
Labarai sun ishe mu cewa gwamnatin Iraki ta bada hutu na musamman domin bada damar aiwatar da wannan tattaki da kuma raya ranar ta arba’in din Imam Hussain (S.a) cikin nasara ba tare da fuskantar kowacce irin matsala ba.
A ta janibin ‘yan uwa almajiran sheikh Ibrahim Zakzaky wadanda ke halartar wannan ibada daga gida najeriya labarai sun tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya kuma sun bi sahun sauran ‘yan uwan su na fadin duniya cikin gudanar da wannan babbar ibada kamar yadda aka saba.
Labarai sun tabbatar da cewa wannan karon maukibin tattakin ya samu halartar babban sha’irin manzon rahama (S) da iyalan gidan sa dinnan watau Sharif Hafiz Abdallah.
Wakilin mu ya bamu labarin cewa sharif hafiz abdallah tare da ‘yan tawagara sun samu halartar tattakin na bana a wani yanayi da yayi kama da babban tarihi wanda ba za’a mance da shi ba.
A wani faifan bidiyo daya zaga kafofin sada zumunta na zamani a hasko shararren sha’irin yana rera baitocin juyayin Imam Hussain (S.a) cikin yanayin juyayi kuma sanya da bakaken kaya wadanda ke alamta yananyin juyayi.
Wannan wata babbar nasara ce wacce dama an saba samun ta a munasabar tattakin, duba da cewa sharif hafiz abdallah dan darikar tijjaniyya ne wanna yake tabbatar da cewa tattakin Imam Hussain (S.a) ba na ‘yan shi’a bane kadai.
Tattakin Imam Hussain na kowanne musulmi ne har ma da kiristoci dama masu rajin kare hakkokin dan adam ko daga kowacce irin fahimta da addinai ma, indai mutum yana da dan adamtaka tattakin Imam Hussain (S.A) nashi ne kuma lamurra na zahiri na tabbatar da hakan.