Kwamitin Tuntuba kan Gaza wanda mambobin Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta OIC suka kafa tare da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, sun haɗu don tattauna matakan haɓaka zamowar Falasɗinu ƙasa mai ‘yanci, da ƙara matsin lamba kan Isra’ila da ƙawayenta.
Majiyoyin diflomasiyya sun ce taron, wanda aka yi a babban birnin Saudiyya na Riyadh ya kawo ƙarshe, inda wakilai suka tattauna matakan da za su ɗauka yayin taron ƙoli na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi na OIC mai zuwa, wanda za a yi a birnin Banjul na Gambiya, ranar 4 ga Mayu.
Minista Fidan zai ci gaba da tattaunawarsa da ƙasashen duniya a Riyadh har zuwa Litinin, a cewar majiyar.
Ƙoƙarin zaman lafiya mai ɗorewa
An shirya Fidan zai gana da takwaransa na Jordan, Ayman Safadi, da na Norway, Espen Barth Eide, da na Yemen, Shai Muhsin Zindani, da kuma jagoran manufofin ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Joseph Borrell.
An kafa Kwamitin Tuntuba kan Gaza lokacin wani taron ƙoli na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, a watan Nuwamba don kawo ƙarshen rikicin Gaza, da taimakawa cimma zaman lafiya mai ɗorewa.
Isra’ila tana ƙaddamar da ƙazamin yaƙin kan Gaza, tun bayan harin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ƙaddamar ranar 7 ga Oktoban bara.
DUBA NAN: Amurka Tace Babu Ruwan Ta Idan Isra’ila Ta Tsokano Iran
Hare-haren sojin Isra’ila, wanda ya kashe Falasɗinawa 34,000 tun lokacin, inda hakan ya mayar da yankin da ke zaman matsugunin mutane miliyan 2.3, ya koma kufai, kuma ya janyo mafi yawancin farar hula suna fuskantar yunwa.