Kwamitin Tsaron MDD Na Kebabben Zama Game Da Batun Mali.
Kwamitin tsaron MDD, na wani kebabben zama yau Talata, domin tattauna halin da ake ciki a Mali, tun bayan da faransa da kawayenta suka yunkuri anniyar janje dakarunsu daga kasar.
Taron wanda faransa ta kira, yayinsa za’a tattauna tasirin janyewar dakarun a kasar ta mali, musaman kan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali (Minusma).
Babban abunda damuwar da ake da ita shi ne makomar tawagar ta MINISMA, wacce ta dogara da tallafin dakarun na faransa.
A cewar jami’an diflomasiyya, janyewar Faransa na iya sa tawagar Turai da ke cikin Minusma, kamar na Jamus Burtaniya suma su janye.