Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Kira Taron Gaggawa Kan Rikicin Ukrain.
Kasashen Amurka Faransa da birtaniya sun bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ya kira zaman gaggawa kan rikicin kasar Ukrain bayan da kasar Rasha ta amince da yancin cin gashin kai ga wasu yankuna biyu da ke Gabashin kasar Ukrain
Zaman ya zo ne bayan kasar Ukrain da Amurka da wasu kasashe guda 6, kasar Rasha da ke rike da jagorancin karba karba na kwamitin ta sanya lokacin da zaa yi zaman, sai dai bata yi Karin haske ko za’a yi zama a fili ba ne ko kuma ba Sirri.
Yanzu haka dai kasar Rasha it ace ke rike da shugabancin karba-karba na Kwamitin tsaro na majalisar dinkiin duniya kuma ita ke da alhakin sanar da lokacin gudanar da taron
Rasha ta dauki matakin amincewa da yancin cin gashin kai na yankunan biyu da ke gabashin kasar Ukrain kuma ta umarci sojojinta da su kaddamar da shirin tabbatar da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya yi kamari