Bayan an kwashe watanni biyar Isra’ila tana yaƙi a Gaza, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a karon farko ya amince a tsagaita wuta nan-take bayan Amurka ta janye daga kaɗa ƙuri’a.
Dukkan ƙasashe 14 mambobin kwamitin tsaro sun amince a tsagaita wuta “nan-take” a watan Ramadan yayin ƙuri’ar da suka kaɗa ranar Litinin, lamarin da sa aka kaure da tafi a zauren majalisar.
Ƙudurin ya yi buƙaci dukkan ɓangarorin su tsagaita wuta “nan-take a watan azumin Ramadan abin da ake fatan zai kai ga tsagaita wuta ta dindindin.”
Kazalika ƙudurin ya yi kira a “gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharaɗi ba, tare da tabbatar da isar kayan agajin jinƙai na magunguna da sauransu” yankin Gaza.
Haka kuma ƙudurin ya buƙaci ɓangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar sakin mutanen da ke tsare a ƙarƙashin dokokin duniya.
A wani labarin na daban shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya taya ɗan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi, 24 ga watan Maris.
“Ina yabawa game da yadda aka yi zaɓen shugaban ƙasa na ranar 24 ga watan Maris, 2024 ba tare da matsala ba kuma ina taya murna ga wanda ya yi nasara, Mr. Bassirou Diomaye Faye, wanda alamu suka nuna cewa shi zai yi nasara. Wannan nasara ce da dimokuraɗiyyar Senegal,” in ji Sall a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.
Sall ya fitar da saƙon ne jim kaɗan bayan tsohon Firaministan Senegal kuma ɗan takarar gamayyar jam’iyyu masu mulki ya amsa shan kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa.
Amadou Ba, ɗan takarar jam’iyya mai mulki ya faɗa a wata sanarwa daga ofishin kamfe ɗinsa ranar Litinin, cewa yana taya murna ga ɗan takarar jam’iyyar adawa, Bassirou Diomaye Diakhar Faye, kuma yana yi masa fatan alheri.
Sakamakon farko ya nuna cewa Faye ya samu aƙalla kashi 57 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Ba ya samu kashi 31.
Nasarar da ya samu a zagayen farko na zaɓen ta dace da abin da aka gani na yadda mutanen ƙasar ke nuna ɓacin-ransu da rashin aikin-yi da shugabanci nagari a ƙasar da ke Yammacin Afirka.
Diomaye Faye, wanda ke da goyon baya daga shahararren ɗan adawa Ousmane Sonko, ya sha alwashin raba Senegal da rashawa a ɓangaren gwamnati.
Watannin tararrabi
Zaɓen da ya gudana ranar Lahadi ya biyo bayan watannin da aka kwashe ana tararrabi da rashin zaman lafiya bayan da shugaba mai ci, Macky Sall ya yi yunƙurin dakatar da zaɓe har zuwa ƙarshen shekara.
DUBA NAN: Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Senegal
Zanga-zangar da ta biyo bayan yunƙurin ta girgiza kyakkyawan sunan da Senegal take da shi a matsayin tsayayyiyar ƙasar dimukurɗiyya a yankin da ya sha fama da jerin juyin mulki a ƴan shekarun nan.