A yayin ziyarar aiki gami da baje kolin kayayakin ayyukan tsaron ruwa a birnin Doha na kasar Qatar, kwamandan sojin ruwan Jamhuriyar musulunci ta Iran Rear Admiral Ali Reza Tasgiri ya tabbatar da cewa, gwamnatin Jamhuriyar musulunci ta Iran a shirye take tsaf domin tabbatar da cikakken tsaro a tekun fasha.
Kwamandan wanda ya jagoranci wasu tawagar sojoji wadanda suka halarci taron wanda ake gudanarwa duk bayan shekara biyu a birnin na Doha kuma karkashin kulawar sarkin Qatar.
Taron wanda ake gudanarwa daga ranar ranar 21 zuwa 23 ga wata maris an gudanar dashi ne a babban tdakin taron ma’aikatara tsaron qatar kuma ma’aikatar tsaon ta qatar ce ta shirya kuma ta nauki nauyi tare da zama mai masaukin baki.
Kamar yadda kwamandan, Rear Admiral Tangsiri ya bayyana anyi amfani da wanna dama domin tataunawar samar da fahimtar juna tsakanin kwamandojin sojin kasashen musulmi domin samar da yanayi mai kyau a tsakani.
Lura da matukar kokarin da Jamhuriyar musulunci ta Iran takeyi domin tabbatar da zaman lafiya gami d akwanciyar hankali a tekun fasha, kwamnadan yayi fatan kasashen yakin tekun fasha zasu bada hadin kai ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran din domin cigaba da samun wannan ingantaccen zaman lafiya a yankin.
”A kullum Jamhuriyar musulunci ta Iran tana kokarin tabbatar da zaman lafiya gami da kwanciyar hankali a yankin tekun fasha gami da mashigar Hormuz, kwamandan ya tabbatarwa mahalarta taron wadanda suka fito daga kasashe mabambanta”
Kwamandan ya kuma bawa hadin kan da kasashen musulmin yankin ke baiwa Iran din wajen aiwatar da ayyukan ta kuma yayi kira ga kasashen na musulmi dasu cigaba da bada cikakken goyon bayan su domin cigaban tsaro a yankin.
Tasghri ya kuma bayyana gamsuwar sa kan yadda Iran ta samu damar wadatuwa da kayan tsaro na zamani da kuma karfin tsaro a yankin na tekun fasha.