Akasarin masoya wasan kwallon kafa sun goyi bayan a rika gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasa da duk bayan shekaru 4 a cewar sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta wallafa a yau Alhamis.
Sakamakon binciken ya nuna cewa kaso 30 sun goyi bayan a gudanar da gasar duk bayan shekaru 2, a yayin da kaso 11 ke goyon bayan gudanar da gasar duk bayan shekaru 3.
Sai dai rahoton ya nuna cewa ra’ayoyin sun danganta ne da shekarun wadanda suka kada kuri’ar da kuma yankunan da suka fito.
Akasarin wadanda suka nuna goyon baya a gudanar da gasar a kasa da bayan shekaru 4 matasa ne a dukkannin yankunan da aka gudanar da binciken, a yayin da datawa ke goyon bayan a ci gaba da gudanar da gasar duk bayan shekaru 4 kamar yadda take tun lokacin da aka fara ta a shekarar 1930.
Nan gaba za a fadada wannan bincike zuwa kan mutane dubu 100.
A cikin shekarun 1990s ne aka yi wa FIFA wannan tayi na gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru 2, kuma a watan Maris ne tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger, wanda shine shugaban sashen bunkasa kwallon kafa na hukumar a yanzu ya tada batun.