Majalisar Dinkin Duniya tace barkewar cutar kwalara da aka samu a kasar Kamaru tsakanin watan Octobar bara zuwa bana tayi sanadiyar mutuwar mutane 154 daga cikin sama da 8,200 da suka harbu da ita.
Cutar kwalara wadda ke haifar da amai da gudawa da kuma hallaka jama’a cikin sa’o’i muddin ba su samu taimakon likita ba na barkewa a kasar Kamaru lokaci zuwa lokaci.
Ofishin jinkai na Majalisar ya ce alkaluman da hukumomin lafiyar Kamaru suka gabatar sun nuna cewar mutane 8,241 suka harbu da cutar daga watan Oktoban bara zuwa Mayu, yayin da 154 suka rasa rayukan su.
Rahotan yace an samu cutar ne a yankuna guda 7 daga cikin 10 dake kasar, inda a Yankin Kudu maso Yamma aka samu mutane 5,628 da suka harbu, yayin da 90 suka mutu, sai kuma Yankin Littoral da ya samu mutane 2,208 da suka harbu, kuma 58 sun mutu.
Karen Perrin, shugaba ofishin Jinkai na OCHA yace samun damar shiga Yankin Kudu maso Yamma na da wahala saboda rikicin Yan awaren da ake fama da shi.
A wani labarin na daban kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata biyar na kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF a Arewa mai Nisa da ke kasar Kamaru, yankin da ke fama da matsalar ‘yan tada kayar baya.
Kungiyar likitocin da kuma wani babban jami’in yankin na Arewa mai Nisa a Kamarun sun lamarin ya auku ne a Alhamis da ta gabata, inda wasu mutane dauke da makamai a Fotokol, kusa da kan iyaka da Najeriya, a suka shiga wani gini da MSF ke amfani da shi, suka kuma sace jami’ai 5.
Mutanen da aka yi garkuwa da su, sun hada da ma’aikatan agaji uku da suka fito daga kasashen Chadi, Senegal da Ivory Coast, da kuma jami’an tsaron Kamaru biyu.
Yankin Arewa mai nisa a Kamaru da ke fama da matsalolin tsaro ya yi iyaka da Najeriya daga bangaren yammacinsa, yayin da kuma daga bangaren gabashi yayi iyaka da kasar Chadi, wadanda su ma suke fafutukar murkushe hare-haren ‘yan ta’adda.